14 “Ka ji wannan, ya Ayuba, Tsaya ka tuna da ayyukan Allah masu banmamaki.
14 “Ka saurari wannan Ayuba; ka tsaya ka dubi abubuwan al’ajabi na Allah.
Abubuwan banmamaki ne Ubangiji yake aikatawa! Duk waɗanda suke murna da su Suna so su fahimce su.
Sai Musa ya ce wa jama'a, “Kada ku tsorata, ku tsaya cik, ku ga ceton Ubangiji, wanda zai yi muku yau, gama Masarawan nan da kuke gani yau, ba za ku ƙara ganinsu ba faufau.
“Amma Ubangiji yana cikin tsattsarkan Haikalinsa, Bari duniya ta yi tsit a gabansa.”
“Ka tuna ka girmama aikinsa, Wanda mutane suke yabo.
Ya ce, “Ku yi shiru, ku sani ni ne Allah, Maɗaukaki ne cikin sauran al'umma, Maɗaukaki kuma a duniya!”
Ba za mu iya fahimtar manyan abubuwa da yake yi ba, Al'ajabansa kuwa ba su da iyaka.
Muryar tsawar Allah mai banmamaki ce, Yana aikata manyan abubuwa da suka fi ƙarfin ganewarmu.
Allah yakan aiko da ruwan sama ya shayar da duniya, Saboda tsautawa, ko saboda ƙasa, ko saboda ƙauna.
Koka san yadda Allah yakan ba su umarni, Ya sa walƙiyar girgijensa ta haskaka?
Ko kuma ka san yadda gizagizai suke tsaye daram a sararin sama? Ayyukan banmamaki na Allah, cikakken masani!
Ka yi tunanin aikin Allah, Wa ya isa ya miƙe abin da ya tanƙware?