11 Yakan cika girgije mai duhu da ruwa, Gizagizai sukan baza walƙiyarsa.
11 Yana cika gizagizai da lema; yana baza walƙiyarsa ta cikinsu.
Yana magana ke nan sai ga wani gajimare mai haske ya zo ya rufe su. Aka kuma ji wata murya daga cikin gajimaren, ta ce, “Wannan shi ne Ɗana ƙaunataccena, wanda nake farin ciki da shi ƙwarai. Ku saurare shi.”
Ubangiji ya ce mini “Zan duba daga samaniya a hankali kamar yadda raɓa take saukowa a natse da gumin dare a lokacin girbi, hasken rana kuma a yini.
Ya cika hannunsa da walƙiya, Yakan sa ta faɗa a kan abin da ya bārata.
Allah ne ya cika gizagizai masu duhu da ruwa, Girgijen kuwa bai kece ba.
Sa'ad da ya ba da umarni ga ruwan sama, Da kuma hanyar da tsawa za ta bi,
Yakan sako ta a ƙarƙashin samaniya duka, Walƙiyarsa takan zagaya dukan kusurwoyin duniya.
Koka san yadda Allah yakan ba su umarni, Ya sa walƙiyar girgijensa ta haskaka?
Sai Ahab ya haura don ya ci ya sha, Iliya kuwa ya hau can ƙwanƙolin Karmel, ya zauna ƙasa, ya haɗa kai da gwiwa.