Sa'ad da na ji, sai jikina ya yi rawa, Leɓunana suka raurawa. Ƙasusuwana suka ruɓe, sai na yi rawar jiki. Zan yi shiru in jira ranar wahala da za ta zo A kan waɗanda suka kawo mana yaƙi.
Ubangiji ya ce, “Ba za ku ji tsorona ba? Ba za ku yi rawar jiki a gabana ba? Ni ne na sa yashi ya zama iyakar teku, Tabbatacciyar iyaka, wadda ba ta hayuwa, Ko da yake raƙuman ruwa za su yi hauka, ba za su iya haye ta ba, Ko da suna ruri, ba za su iya wuce ta ba.
A safiyar rana ta uku aka yi tsawa, da walƙiyoyi, da girgije mai duhu a bisa dutsen, aka tsananta busar ƙaho, sai dukan jama'ar da suke cikin zango suka yi rawar jiki.