8 Amma idan aka ɗaure su da sarƙoƙi, Da kuma igiyar wahala,
8 Amma in mutane suna daure da sarƙoƙi, ƙunci kuma ya daure su,
Waɗansu suna zaune cikin duhu da inuwar mutuwa, 'Yan sarƙa suna shan wahala da sarƙoƙi,
Zunuban mutum tarko ne, komar zunubinsa ce take kama shi.
Ya toshe hanyata da sassaƙaƙƙun duwatsu, Ya karkatar da hanyoyina.
Mutuwa ta ɗaure ni da igiyarta tam, Razanar kabari ta auka mini, Na cika da tsoro da alhini.
Mutuwa ta ɗaure ni kam da igiyoyinta, Kabari kuma ya ɗana mini tarko.
Ba ku iya ganin abin da Allah ya yi mini, Ya kafa tarko don ya kama ni.
Ka ɗaure ƙafata da sarƙoƙi, Kakan lura da kowace takawata, Har kana bin diddigin sawayena.
Zai kuɓutar da waɗanda suke shan tsanani, Ta wurin tsananin da suke sha, Yakan buɗe kunnuwansu ta wurin shan wahala.
Ka lura kada ka rinjayu a kan aikata mugunta, Gama saboda haka kake shan wannan tsanani, Don a tsare ka daga aikata mugunta.
Mugaye sun ɗaure ni tam da igiyoyi, Amma ba zan manta da dokarka ba.
Su ɗaure sarakunansu da sarƙoƙi, Su ɗaure shugabanninsu da sarƙoƙin baƙin ƙarfe,