Duk da haka kuwa bai taɓa barin kansa, ba shaida ba, domin yana yin alheri, shi da yake yi muku ruwan sama, da damuna mai albarka, yana ƙosar da ku da abinci, yana kuma faranta muku rai.”
Sai Sama'ila ya roƙi Ubangiji, Ubangiji kuwa ya sa aka yi tsawa da ruwan sama a wannan rana. Dukan jama'a kuwa suka ji tsoron Ubangiji da Sama'ila ƙwarai.
A sa'ad da Sama'ila yake miƙa hadaya ta ƙonawa, Filistiyawa suka matso don su yi yaƙi da Isra'ilawa, sai Ubangiji ya buge wa Filistiyawa tsawa mai ƙarfi daga sama, suka kuwa ruɗe suka juya a guje.
Za a hallakar da maƙiyan Ubangiji, Zai yi musu tsawa daga Sama. Ubangiji zai hukunta dukan duniya, Zai ba sarkinsa iko, Zai sa zaɓaɓɓen sarkinsa ya zama mai nasara.”
Sa'ad da suke gudun Isra'ilawa suna a gangarar hawan Bet-horon, sai Ubangiji ya jefe su da manyan duwatsu daga sama, har zuwa Azeka, suka mutu. Waɗanda suka mutu ta ƙanƙarar duwatsu sun fi waɗanda Isra'ilawa suka kashe da takobi.
Ubangiji ya bishe ku cikin babban jejin nan mai bantsoro, ƙasa mai macizai masu zafin dafi, da kunamai, da busasshiyar ƙasa wadda ba ta da ruwa. Ubangiji kuwa ya ba ku ruwa daga dutsen ƙanƙara.
Ku tuna yadda Ubangiji Allahnku ya bishe ku shekarun nan arba'in a jeji don ya koya muku tawali'u. Ya jarraba ku don ya san zuciyarku, ko za ku kiyaye umarnansa ko babu.