Amma hikimar nan ta Sama, da farko dai tsattsarka ce, mai lumana ce, saliha ce, mai sauƙin kai, mai tsananin jinƙai, mai yawan alheri, mai kaifi ɗaya, sahihiya kuma.
Kowace kyakkyawar baiwa, da kowace cikakkiyar kyauta, daga Sama suke, sun sauko ne daga wurin Uban haskoki, wanda ba sauyawa ko wata alamar sākewa a gare shi faufau.
Suna raira waƙar da Musa bawan Allah ya yi, da kuma wadda ake yi wa Ɗan Ragon nan, suna cewa, “Ayyukanka manya ne, masu banmamaki, Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki! Hanyoyinka na adalci ne, na gaskiya ne kuma, Ya Sarkin al'ummai.
Domin haka Ubangiji ya shirya bala'i, ya kuma aukar mana da shi, gama Ubangiji Allahnmu mai adalci ne cikin dukan abin da ya aikata, amma mu ba mu bi maganarsa ba.
Ya Ubangiji, kai mai adalci ne, amma mu sai kunya, kamar yadda yake a yau ga mutanen Yahuza, da mazaunan Urushalima da dukan Isra'ilawa, waɗanda suke kusa da waɗanda suke nesa a dukan ƙasashen da ka kora su saboda rashin amincin da suka yi maka.
“Shi Dutse ne, aikinsa kuma cikakke ne, Gama dukan hanyoyinsa masu adalci ne. Allah mai aminci ne, babu rashin gaskiya a gare shi, Shi mai adalci ne, nagari ne kuma.
A Ranar Shari'a Sarauniyar Kudu za ta tashi tare da mutanen zamanin nan, ta kā da su, don ta zo ne daga bangon duniya ta ji hikimar Sulemanu. Ga kuma wanda ya fi Sulemanu a nan.
Ya Ubangiji, kai adali ne sa'ad da na kawo ƙara a gare ka. Duk da haka zan bayyana ƙarata a gabanka, Me ya sa mugaye suke arziki cikin harkarsu? Me ya sa dukan maciya amana suke zaman lafiya, Suna kuwa ci gaba?
Sai Elihu, ɗan Barakel, mutumin Buz, daga cikin iyalin Arama, ya husata, yana fushi da Ayuba saboda ya baratar da kansa, bai bari Allah ya baratar da shi ba.