Suna raira waƙar da Musa bawan Allah ya yi, da kuma wadda ake yi wa Ɗan Ragon nan, suna cewa, “Ayyukanka manya ne, masu banmamaki, Ya Ubangiji Allah Maɗaukaki! Hanyoyinka na adalci ne, na gaskiya ne kuma, Ya Sarkin al'ummai.
Yanzu ni, Nebukadnezzar, ina yabon Sarkin Samaniya, ina ɗaukaka shi, ina kuma girmama shi saboda dukan ayyukansa daidai ne, al'amuransa kuma gaskiya ne. Yakan ƙasƙantar da masu girmankai.”
Amma zan raira waƙa a kan ikonka, Kowace safiya zan raira waƙa da ƙarfi Ga zancen madawwamiyar ƙaunarka. Kai mafaka ne a gare ni, Wurin ɓuya a kwanakin wahala.
Ku lura fa, sa'ad da kuka dubi sama, kuka ga rana, da wata, da taurari, da dai dukan rundunar sama, don kada fa ku jarabtu, ku yi musu sujada, ko ku bauta musu. Ubangiji Allahnku ya sa waɗannan saboda dukan al'ummai.
Musa da jama'ar Isra'ila suka raira wannan waƙa ga Ubangiji suka ce, “Zan raira waƙa ga Ubangiji, gama ya ci gawurtacciyar nasara, Dawakai da mahayansu ya jefar cikin bahar.