Zinariyarku da azurfarku sun ɓāci ƙwarai, ɓācin nan nasu kuwa zai zama shaida a kanku, yă ci naman jikinku kamar wuta! Kun dai jibge dukiya a zamanin ƙarshen nan!
Azurfarsu da zinariyarsu ba za su cece su A ranar hasalar Ubangiji ba, A cikin zafin kishinsa Dukan duniya za ta hallaka. Zai kawo ƙarshen duniya duka nan da nan.
Mala'ikan Ubangiji kuwa ya shiga sansanin Assuriyawa ya kashe sojoji dubu ɗari da dubu tamanin da dubu biyar (185,000). Da asuba ta yi, sai ga su can kwankwance, duk sun mutu!