Allah Mai Tsarki na Isra'ila, Ubangiji, wanda ya fanshe ku, ya ce, “Ni ne Ubangiji Allahnku, Wanda yake so ya koya muku domin amfanin kanku, Ya kuwa nuna muku hanyar da za ku bi.
Amma Ubangiji ya faɗakar da jama'ar Isra'ila da jama'ar Yahuza ta bakin annabawa da kowane maigani, cewa su bar mugayen hanyoyinsu, su kiyaye umarnansa da dukan dokokinsa waɗanda ya umarci kakanninsu da su, waɗanda kuma ya aiko musu ta wurin bayinsa annabawa.
Ɗaya daga cikin masu sauraronmu wata mace ce, mai suna Lidiya, mai sayar da jar hajja, mutuniyar Tayatira, mai ibada ce kuma. Ubangiji ya buɗe zuciyarta, har ta mai da hankali ga abin da Bulus ya faɗa.
Na sani ba za a iya gaskata ku ba, Tun daga haihuwarku kuma an san ku da tayarwa. Shi ya sa ba ku taɓa jin wannan ba ko kaɗan, Ko kalma ɗaya ba ta taɓa shiga kunnenku ba.
Ba ka bukatar baye-baye da hadayu, Ba ka so a miƙa maka hadayun ƙonawa Na dabbobi a bisa bagade ba, Ko baya-baye don a kawar da zunubai. A maimakon haka, ka ba ni kunnuwan da zan saurare ka.
Na ce, hakika za ka ji tsorona, Ka kuma karɓi horo. Ba za a rushe wurin zamanta ba Bisa ga hukuncin da na yi mata. Amma suka ɗokanta su lalatar da ayyukansu.