Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayuba 35:13 - Littafi Mai Tsarki

13 Hakika Allah bai ji holoƙon kukansu ba, Allah Mai Iko Dukka kuwa bai kula da shi ba.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

13 Lalle Allah ba ya sauraron roƙonsu na wofi; Maɗaukaki ba ya kula da roƙonsu.

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayuba 35:13
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Sa'ad da mutanen kirki sukan yi addu'a, Ubangiji yakan kasa kunne, amma ba ya kulawa da mugaye.


Saboda haka ni Ubangiji na ce, ‘Ga shi, ina kawo musu masifa wadda ba za su iya tsere mata ba, ko da za su yi kuka gare ni ba zan ji su ba.


“Sa'ad da kuke ɗaga hannuwanku wajen yin addu'a, ba zan dube ku ba. Kome yawan addu'ar da kuka yi, ba zan kasa kunne ba domin zunubi ya ɓata hannuwanku.


Kukan yi addu'a ku rasa, don kun yi ta da mugun nufi ne, don ku ɓatar a kan nishaɗinku.


“In kuwa kuna addu'a, kada ku yi ta maimaitawar banza, kamar yadda al'ummai suke yi, a zatonsu za a saurare su saboda yawan maganarsu.


Sa'ad da kuka kawo mini hadayun ƙonawa Da hadayunku na tsaba, ba zan karɓa ba. Ba kuma zan karɓi turkakkun dabbobinku Waɗanda kuka miƙa mini hadayun godiya ba.


Ba su yi kuka gare ni da zuciya ɗaya ba, Sa'ad da suke kuka a gadajensu, Sun tsattsaga jikinsu domin abinci da ruwan inabi. Sun yi mini tawaye.


Idan ka ƙi biyayya ga doka, Allah zai ƙi jin addu'o'inka.


Ubangiji yana murna sa'ad da adalai suke yin addu'a, amma yana ƙin hadayun da mugaye suke miƙa masa.


Zai saurari jama'arsa wadda ya rabu da ita, Zai kuwa ji addu'arta.


“Na yi kira gare ka, ya Allah, amma ba ka amsa mini ba, Na yi addu'a kuma, amma ba ka kula da ni ba.


Mun sani Allah ba ya sauraron masu zunubi, amma duk wanda yake mai bautar Allah, yake kuma aikata nufinsa, Allah yakan saurare shi.


Idan wauta tasa ta kai shi ga dogara ga mugunta, To, mugunta ce kaɗai zai samu.


Sa'an nan za su yi kuka ga Ubangiji, Amma Ubangiji ba zai amsa musu ba. Zai ɓoye musu fuskarsa a wannan lokaci, Saboda mugayen ayyukansu.


Da ban watsar da zunubaina ba, Da Ubangiji bai ji ni ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ