Kun ce, ‘Ba amfani a bauta wa Ubangiji. Ina amfani a kiyaye abin da ya ce, ko mu yi ƙoƙarin nuna cewa zuciyarmu ta ɓāci saboda ayyukan da muka yi wa Ubangiji Mai Runduna.
Mutane sukan ce, “Me ya sa muka yi azumi, Ubangiji bai gani ba? Me ya sa muka ƙasƙantar da kanmu, Ubangiji kuwa bai kula ba?” Ubangiji ya ce musu, “Duba, a ranar da kuke azumi, nishaɗin kanku kuke nema, kuna zaluntar dukan ma'aikatanku.