7 “Wane irin mutum ne kai, Ayuba, Da kake shan raini kamar yadda kake shan ruwa,
7 Wane mutum ne kamar Ayuba, wanda yake shan ba’a kamar ruwa?
Mutum yakan sha mugunta kamar yadda yake shan ruwa, Hakika mutum ya lalace, ya zama mai rainako.
Ta ce, “Wawayen mutane! Har yaushe za ku yi ta kasancewa haka? Har yaushe za ku daina jin daɗin yi wa mai ilimi ba'a? Faufau ba za ku taɓa koya ba?
Idan wani mutum ya ji zantuttukan la'anan nan sa'an nan ya sa wa kansa albarka a zuciyarsa, yana cewa, ‘Ba abin da zai same ni ko na bi taurin zuciyata,’ wannan zai haddasa lalacewar ɗanye da busasshe gaba ɗaya.
Mugunta da ta'adi kamar ci da sha suke a gare su.
Har abokaina ma, suna ta yi mini dariya yanzu, Suna ta dariya ko da yake ni adali ne marar laifi, Amma akwai lokacin da Allah ya amsa addu'o'ina.
Ba gaskiya ga mashaidin da ya yi niyyar cutar wani. Mugaye suna ƙaunar yin mugunta.
Ayuba, kana tsammani ba za mu iya ba ka amsa ba? Kana tsammani maganganunka na ba'a Za su sa mu rasa abin da za mu mayar maka?
“Ka damu ƙwarai don ka ga an hukunta mugaye, Amma hukunci da adalci sun kama ka.