5 Gama Ayuba ya ce, ‘Ni marar laifi ne, Amma Allah ya ƙwace mini halaliyata.
5 “Ayuba ya ce, ‘Ba ni da laifi, amma Allah ya hana mini hakkina.
Ka ce kai tsattsarka ne, ba ka da laifi, Kai tsabtatacce ne, ba ka da wata ƙazanta.
“Na rantse da Allah Mai Iko Dukka, Wanda ya ƙwace mini halaliyata, Wanda ya ɓata mini rai.
Mutanen nan uku sun daina ba Ayuba amsa, saboda yana ganin kansa adali ne.
Adalci shi ne suturata, Gaskiya ita ce rigata da rawanina.
Amma ban yi wani aikin kama-karya ba, Addu'ata ga Allah kuwa ta gaskiya ce.
Ka ɗauka duk abin da kake faɗa gaskiya ne, Ka kuma mai da kanka kai mai tsarki ne a gaban Allah.
Ka sani, ba ni da laifi, Ka kuma sani, ba wanda zai cece ni daga gare ka.
Shi ya aiko da hadura, suka yi kacakaca da ni, Suka ƙuƙƙuje ni, ga shi kuwa, ba wani dalilin da ya sa ya yi mini rauni.
Kai, kun zaƙe, ku daina aikata rashin adalci, Kada ku sa mini laifi, nake da gaskiya.
A shirye nake in faɗi ƙarata, Domin na sani ina da gaskiya.
Bari mu zaɓi abin da yake daidai, Bari kuma mu daidaita abin da yake mai kyau tsakanin junanmu.
Isra'ila, me ya sa kake gunaguni, Cewa Ubangiji bai san wahalarka ba, Ko ya kula ya daidaita abubuwa dominka?
Allah bai taɓa yin danniya ba, Bai kuma taɓa fāsa aikata abin da yake daidai ba.
Na ce ban yarda da kama-karyarsa ba, Amma ba wanda ya kasa kunne. Na nema a aikata gaskiya, amma sam, babu.