Zan ɗauka fushin Ubangiji ne, Gama na yi masa zunubi, Sai lokacin da ya ji da'awata, Har ya yanke mini shari'a. Zai kawo ni zuwa wurin haske, Zan kuwa ga cetonsa.
Sai Bal'amu ya ce wa mala'ikan Ubangiji, “Na yi zunubi, gama ban sa ka tsaya a hanya don ka tarye ni ba. Yanzu fa, idan ka ga mugun abu ne, to, sai in koma.”
Na kula sosai, na saurara, Amma ba wanda ya faɗi wata maganar kirki, Ba wanda ya taɓa barin muguntarsa, Kowa cewa yake, “Me na yi?” Kamar dokin da ya kutsa kai cikin fagen fama.