Don haka, kada ku yanke wani hukunci tun lokaci bai yi ba, kafin komowar Ubangiji, wanda zai tone al'amuran da suke ɓoye a duhu, ya kuma bayyana nufin zukata. A sa'an nan ne, Allah zai yaɓa wa kowa daidai gwargwado.
Waɗanda suke ƙoƙarin ɓoye wa Ubangiji shirye-shiryensu sun shiga uku! Suna gudanar da dabarunsu a ɓoye, suna tsammani ba wanda zai gan su ko ya san abin da suke yi.