2 “Ku mutane masu hikima, ku ji maganata, Ku kasa kunne ga abin da zan faɗa, ku masana.
2 “Ku ji maganata, ku masu hikima; ku saurare ni, ku masu ilimi.
Ya ku 'yan'uwa, kada ku yi hankali irin na yara, sai dai a wajen mugunta, ku yi halin jarirai, amma a wajen hankali ku yi dattako.
Waɗannan karin magana sukan ƙara wa masu ilimi hikima, sukan zama jagora ga masana,
Ina magana da ku a kan ku mahankalta ne fa, ku duba da kanku ku ga abin da nake faɗa.
Elihu ya ci gaba.
Kunne yake rarrabewa da magana, Kamar yadda harshe yake rarrabewa da ɗanɗanar abinci.