Za ka yi zuffa da aiki tuƙuru kafin ka sami abinci, har ka koma ƙasa, gama da ita aka siffata ka, kai turɓaya ne, ga turɓaya kuma za ka koma.” (2Tas 3.10; Far 2.7; Zab 90.3; 104.29; M.Had 12.7)
Duk taliki wanda yake motsi bisa duniya ya mutu, da tsuntsaye, da dabbobin gida, da na jeji, da dukan masu rarrafe waɗanda suke rarrafe bisa duniya, da kowane mutum,
Dukanmu mutuwa za mu yi, kamar ruwan da ya zube a ƙasa, wanda ba ya kwasuwa, haka za mu zama. Allah ba yakan ɗauke rai kurum ba, amma yakan shirya hanya domin wanda ya shuɗe ba zai ɓata daga gabansa ba.