Don lalle ne a gabatar da mu duka, a gaban kursiyin shari'a na Almasihu, domin kowa yă sami sakamakon abin da ya yi tun yana tare da wannan jiki, ko mai kyau ne, ko kuma marar kyau.
Mai yiwuwa ne ka ce kai ba ruwanka, amma Allah ya sani, yana kuwa auna manufofinka. Yana lura da kai, ya kuwa sani. Yakan sāka wa mutane a kan abin da suke aikatawa.
Bisa ga ayyukansu, haka zai sāka musu hasala, a kan maƙiyansa kuwa ramawa, a kan abokan gābansa, zai rama, da kuma a kan ƙasashen da suke a bakin gāɓa.
yana ba da bashi da ruwa da ƙari, wannan ba zai rayu ba, gama ya aikata dukan abubuwan nan masu banƙyama. Zai mutu lalle, alhakin jininsa kuwa yana a kansa.