7 Don haka kada ka razana saboda ni, Abin da zan faɗa maka, ba abin da zai fi ƙarfinka.
7 Kada ka ji tsorona, ba abin da zai fi ƙarfinka.
Wato ka daina hukuncin da kake yi mini, Kada ka sa razanarka ta ragargaza ni.
Ka daina hukunta ni, ya Allah! Ka daina razanar da ni.
Hasalarka ta bi ta kaina, Tasar mini da kake ta yi, ta hallaka ni.
Ka hukunta ni dare da rana, ya Ubangiji, Ƙarfina duka ya ƙare sarai, Kamar yadda laima yake bushewa, Saboda zafin bazara.
“Hakika na ji maganar da ka yi, Na kuwa ji amon maganganunka,
Da a ce Allah mutum ne, Da sai in mayar masa da magana, Da sai mun je ɗakin shari'a a yanka mana shari'a.