4 Ruhun Allah ne ya yi ni, Mai Iko Dukka ya hura mini rai.
4 Ruhun Allah ne ya yi ni; numfashin Maɗaukaki ya ba ni rai.
Amma Ruhun Allah Mai Iko Dukka ne wanda yake cikin mutum, Yakan ba mutane basira.
Sa'an nan Ubangiji Allah ya siffata mutum daga turɓayar ƙasa, a cikin kafafen hancinsa kuwa ya hura numfashin rai, mutum kuma ya zama rayayyen taliki.
Muddin ina numfashi, Ruhun Allah kuma yana cikin hancina
Haka kuma yake a rubuce, “Mutumin farko, Adamu, ya zama rayayyen taliki,” Adamun ƙarshe kuwa Ruhu ne mai rayarwa.
Kai ne ka ba ni rai da madawwamiyar ƙauna, Kulawarka ce ta sa ni rayuwa.
Ubangiji ya halicci duniya da umarninsa, Rana, da wata, da taurari kuma bisa ga maganarsa.
Ka'idar nan ta Ruhu mai ba da rai da yake ga Almasihu Yesu ta 'yanta ni daga ka'idar zunubi da ta mutuwa.
Daidai ne a gare ka ka yi mugunta? Ka wulakanta abin da kai da kanka ka yi? Sa'an nan ka yi murmushi saboda dabarun mugaye?
Allah shi ne yake bi da rayukan talikansa. Numfashin dukan mutane kuwa a ikonsa yake.
Amma sa'ad da ka hura musu numfashi, sai su rayu, Kakan sabunta fuskar duniya.
Allah ya halicci sammai ya kuma shimfiɗa su, Ya yi duniya, da dukan masu rai nata, Ya ba da rai da numfashi ga dukan mutanenta. Yanzu kuwa Ubangiji Allah ya ce wa bawansa,