30 Don ya komo da ran mutum daga kabari, Domin a haskaka shi da hasken rai.
30 Ya juyo da ransa daga fāɗawa cikin rami, don hasken rai ya haskaka a kansa.
Domin ka cece ni daga mutuwa, Ka hana a ci nasara a kaina. Saboda haka a gaban Allah nake tafiya A hasken da yake haskaka wa masu rai.
Ɓacin zuciyata zai juya ya zama salama. Ka ceci raina daga dukan hatsari, Ka gafarta dukan zunubaina.
Allah ya fanshe ni daga gangarawa zuwa kabari, Raina kuwa zai ga haske.’
domin ka buɗe musu ido, su juyo daga duhu zuwa haske, daga kuma mulkin Shaiɗan zuwa wurin Allah, domin su sami gafarar zunubai, da kuma gādo tare da dukan tsarkaka saboda sun gaskata da ni.’ ”
Sai Yesu ya ƙara musu da cewa, “Ni ne Hasken duniya. Wanda yake bi na ba zai yi tafiya a duhu ba, amma zai sami hasken rai,”
Yanzu fa, zuriyar Yakubu, bari mu yi tafiya a cikin hasken da Ubangiji ya ba mu!
Mala'ikan da zai yi masa alheri ya ce, ‘Ka cece shi daga gangarawa zuwa cikin kabari, Na sami abin da zai fanshe shi!’
Yakan hana su zuwa kabari, Ya hana ransu halaka da takobi.
“Haba Ayuba, ka kula fa, ka kasa kunne, Ga abin da nake faɗa, Ka yi shiru, zan yi magana.
Ka dube ni, ya Ubangiji Allahna, ka amsa mini, Ka mayar mini da ƙarfina, don kada in mutu.
Duk da haka zai tarar da kakanninsa waɗanda suka mutu, Inda duhu ya dawwama har abada.
Da umarninsa ya warkar da su, Ya cece su daga kabari.
Ubangiji ya ce, “Ke kuma, saboda jinin alkawarina da yake tsakanina da ke, Zan 'yantar da waɗanda suke cikin rami, Waɗanda aka kama daga cikinki.