Kun matsa wa talakawa lamba, Kun ƙwace musu abincinsu. Saboda haka kyawawan gidajen nan da kun gina da dutse, Ba za ku zauna a cikinsu ba, Ba kuwa za ku sha ruwan inabin nan Daga kyawawan gonakin inabinku ba.
“Isra'ila, na yi niyya in karɓe ku kamar ɗana, In gādar muku da kyakkyawar ƙasa Mafi kyau a dukan duniya. Na zaci za ku ce ni ne mahaifinku, Ba za ku ƙara rabuwa da bina ba.
Matar ta ga yadda itacen yana da kyau, 'ya'yansa kuma kyawawa, abin sha'awa ne kuma ga ido, abin marmari ne domin ba da hikima, ta tsinka daga 'ya'yansa, ta kuwa ci, ta kuma bai wa mijinta waɗansu, shi kuma ya ci.