18 Yakan hana su zuwa kabari, Ya hana ransu halaka da takobi.
18 don a kāre su daga fāɗuwa cikin rami, a kāre su daga hallaka ta wurin takobi.
Ubangiji ba ya jinkirta alkawarinsa, yadda waɗansu suka ɗauki ma'anar jinkiri, amma mai haƙuri ne a gare ku, ba ya so kowa ya hallaka, sai dai kowa ya kai ga tuba.
Don ya komo da ran mutum daga kabari, Domin a haskaka shi da hasken rai.
Allah ya fanshe ni daga gangarawa zuwa kabari, Raina kuwa zai ga haske.’
Ku ɗauki haƙurin Ubangijinmu, ceto ne. Haka ma, ƙaunataccen ɗan'uwanmu Bulus ya rubuto muku, bisa ga hikimar da aka ba shi,
Ko kuwa kana raina yalwar alherinsa, da jimirinsa, da kuma haƙurinsa ne? Ashe, ba ka sani ba alherin Allah yana jawo ka zuwa ga tuba?
Mala'ikan da zai yi masa alheri ya ce, ‘Ka cece shi daga gangarawa zuwa cikin kabari, Na sami abin da zai fanshe shi!’
Yana gab da shiga kabari, Ransa yana hannun mala'ikun mutuwa.
Bai sa zuciya zai kuɓuta daga duhu ba, Gama takobi yana jiransa a wani wuri don ya kashe shi.
Domin ya kawar da su daga aikin da suke yi, Ya kuma kawar musu da girmankai.
Amma idan ba su kasa kunne ba, Za a hallaka su da takobi, Su mutu jahilai.
Ba ta hawan hanyar juna, Kowa tana bin hanyarta. Takan kutsa cikin abokan gāba, ba a iya tsai da ita.