Ko tukunyar yumɓu tana iya gardama da magininta, Tukunyar da take daidai da sauran tukwane? Ko yumɓu ya iya tambayar abin da maginin yake yi? Ko tukunya tana iya gunaguni a kan magininta?
Dukan mazaunan duniya ba a bakin kome suke a gare shi ba. Yakan yi yadda ya nufa da rundunar sama da mazaunan duniya, Ba mai hana shi, ba kuma mai ce masa, ‘Me kake yi?’
Tun da farko na faɗa muku yadda abin zai zama, Tuntuni na yi faɗi a kan abin da zai faru. Na kuwa ce shirye-shiryena ba za su taɓa fāɗuwa ba, Zan aikata dukan abin da na yi niyyar yi.