10 Ka ce Allah ya zarge ka ya ɗauke ka tankar maƙiyansa,
10 Duk da haka Allah ya same ni da laifi; ya ɗauke ni maƙiyinsa,
Allah ya zaburo mini da fushi, Ya maishe ni kamar mafi mugunta daga cikin maƙiyansa.
Gama Ayuba ya ce, ‘Ni marar laifi ne, Amma Allah ya ƙwace mini halaliyata.
“Da a ce ina da wanda zai kasa kunne gare ni, Da sai in sa hannu a kan abin da na faɗa, Allah kuwa Mai Iko Dukka ya amsa mini. “Da ƙarar da maƙiyana suke kai ni, a rubuce ne,
Ka zama mugu a gare ni, Da ƙarfin dantsenka ka tsananta mini.
Allah ya kakkarya gaɓoɓina da fushinsa, Yana dubana da ƙiyayya.
Sa'an nan za ka lura da kowace takawata Amma ba za ka bi diddigin zunubaina ba.
Shi ya aiko da hadura, suka yi kacakaca da ni, Suka ƙuƙƙuje ni, ga shi kuwa, ba wani dalilin da ya sa ya yi mini rauni.
Sai dukan wahalar da nake sha ta yi ta firgita ni, Na sani Allah ya ɗauke ni mai laifi.
Tun da yake Allah ya ɗauka, ni mai laifi ne, To, me zai sa in damu?