Suka aiko almajiransu wurinsa tare da waɗansu mutanen Hirudus, suka ce, “Malam, ai, mun sani kai mai gaskiya ne, sai koyar da tafarkin Allah sosai kake yi, ba ka kuma zaɓen kowa, don ka ɗauki kowa da kowa daidai.
Yowab baranka ya yi wannan don ya daidaita al'amarin. Amma ubangijina yana da hikima irin ta mala'ikan Allah domin ya san dukan al'amuran da suke a duniya.”
Na kuma yi tunani a kan maganar ubangijina, sarki, za ta kwantar da zuciyata, gama ubangijina, sarki, kamar mala'ikan Allah yake, yana rarrabe tsakanin nagarta da mugunta. Ubangiji Allahnka ya kasance tare da kai!”
Kada ku ɓata shari'a, kada ku yi sonzuciya, kada kuma ku karɓi hanci, gama cin hanci yakan makantar da idanun mai hikima, ya karkatar da maganar adali.
Kada ku nuna bambanci cikin shari'a, ko babban mutum ne ko talaka, duka biyu za ku ji su. Kada ku ji tsoron fuskar mutum, gama shari'a ta Allah ce. In kuwa shari'a ta fi ƙarfinku, sai ku kawo ta wurina, ni kuwa zan yanke ta.’
Saboda haka, ni ma zan sa jama'ar Isra'ila su raina ku, su ƙasƙantar da ku a gaban dukan mutane, domin ba ku kiyaye umarnina ba, sa'ad da kuke koyar da nufina, kun yi tara.”