20 Tilas in yi magana don in huce, Dole in ba da amsa.
20 Dole in yi magana in sami lafiya; dole in buɗe baki in ba da amsa.
Ku ba ni zarafi in yi magana, sa'an nan in na gama ku amsa in kun ga dama.
“Ayuba, ka ɓata mini rai, Ba zan yi haƙuri ba, sai na ba ka amsa.
“Ya Allah, za ka yi ƙarata? Idan kuwa ka yi, to, a shirye nake in yi shiru in mutu.
“Ku yi shiru ku ba ni zarafi in yi magana. Duk abin da zai faru, ya faru.
Ga zuciya tana kama da ruwan inabin da ba shi da mafitar iska, Kamar sabuwar salkar ruwan inabi wadda take shirin fashewa.
Ba zan yi wa kowa son zuciya ba, Ko kuma in yi wa wani fādanci.
“Ayuba, za ka ji haushi in na yi magana? Ba zan iya kannewa, in yi shiru ba.