17 A'a, ni kuma zan ba da tawa amsa, In kuma faɗi ra'ayina.
17 Ni ma zan faɗi nawa; ni ma zan faɗi abin da na sani.
“Amma a kan wannan, Ayuba, ka yi kuskure, zan ba ka amsa, Gama Allah ya fi kowane mutum girma.
Don haka na ce ku kasa kunne gare ni, Bari in faɗa muku nawa ra'ayi.
Ni kuma sai in tsaya don ba su ce kome ba? Sun tsaya kurum, don ba su da ta cewa?
Cike nake da magana, Ruhun da ka cikina ya iza ni.