10 Don haka na ce ku kasa kunne gare ni, Bari in faɗa muku nawa ra'ayi.
10 “Saboda haka nake ce muku, ku saurare ni; ni ma zan gaya muku abin da na sani.
Amma a nawa ra'ayi, za ta fi farin ciki, in ta zauna a yadda take. A ganina kuwa ina da Ruhun Allah.
A game da matan da ba su yi aure ba kuwa, ba ni da wani umarnin Ubangiji, amma ina ba da ra'ayina ne a kan ni amintacce ne, bisa ga jinƙan Ubangiji.
Ba tsofaffi ne masu wayo ba, Ba kuma masu yawan shekaru kaɗai yake gane abin da yake daidai ba.
“Ga shi, na dakata na ji maganarku, Na kasa kunne ga maganarku ta hikima, Tun kuna tunani a kan abin da za ku faɗa.