Sai na iske wani abu da ya fi mutuwa ɗaci, wato mace wadda ƙaunar da take yi maka za ta kama ka kamar tarko, kamar kuma raga. Rungumewar da za ta yi maka za ta ɗaure ka kamar sarƙa. Wanda Allah yake jin daɗinsa zai tsere mata, amma za ta kama mai zunubi.
sa'ad da Sulemanu ya tsufa sai suka janye zuciyarsa zuwa bin waɗansu gumaka, bai bi Ubangiji Allahnsa da zuciya ɗaya kamar yadda tsohonsa, Dawuda, ya yi ba.
Shugabannin Filistiyawa, su biyar suka je wurinta suka ce mata, “Ki yi masa kirsa, don ki san dalilin irin ƙarfin nan nasa, da kuma yadda za mu yi maganinsa, mu ɗaure shi don mu rinjaye shi. Kowannenmu zai ba ki shekel dubu da ɗari (1,100).”
Dukansu mazinata ne, Suna kama da tanda da aka zafafa, Wadda matoyi ya daina iza mata wuta, Tun daga lokacin cuɗe kullu Har zuwa lokacin da yisti ya tasar da shi.
Na faɗa musu cewa, “Ba a kan irin wannan ba ne Sulemanu Sarkin Isra'ila ya yi laifi? A al'ummai, ba sarki kamarsa. Allahnsa ya ƙaunace shi, ya sarautar da shi a Isra'ila, duk da haka baren mata suka sa shi ya yi zunubi.
“ ‘Kada ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka. Kada kuma ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka, ko gonarsa, ko barorinsa mata ko maza, ko sansa, ko jakinsa, ko kowane abu da yake na maƙwabcinka.’