Ka faɗa masa, ni Ubangiji, na ce, ‘Ka kashe mutum, kana kuma ƙwace abin da ya mallaka?’ Ka faɗa masa ga abin da na faɗa, ‘A wurin da karnuka suka lashe jinin Nabot, a nan ne kuma karnuka za su lashe jininka.’ ”
Ubangiji yana zuwa ya hukunta jama'arsa a duniya saboda zunubansu. Kashe-kashen da aka yi a duniya a ɓoye, za a bayyana su, ƙasa ba za ta ƙara ɓoye waɗanda aka kashe ba.
Kaiton wanda ya gina gidansa ta hanyar rashin adalci, Benayensa kuma ta hanyar rashin gaskiya. Wanda ya sa maƙwabcinsa ya yi masa aiki a banza, Bai ba shi hakkinsa ba.