38 “Idan ƙasata tana kuka da ni, Ita da kunyoyinta,
38 “In ƙasata tana kuka da ni kunyoyinta duk sun cika da hawaye,
Ga shi kuwa, zaluncin da kuka yi na hakkin masu girbi a gonakinku yana ta ƙara, kukan masu girbin kuwa ya kai ga kunnen Ubangijin Runduna.
Dutse zai yi kuka daga garu, Katako kuwa zai amsa masa daga aikin da aka yi da itace.
Sauruka suna cike da tumaki, Kwaruruka suna cike da alkama, Suna sowa suna raira waƙa ta farin ciki!
Samaniya ta bayyana zunubin wannan mutum, Duniya kuma ta ba da shaida gāba da shi.
“Mugaye sukan ci iyaka, Don su ƙara yawan gonarsu. Sukan saci tumaki su zuba cikin garkunansu.