Zan sa shi ya zama sarki mai cikakken iko, na zuriyar Dawuda. Mabuɗan fāda suna hannunsa, abin da ya buɗe, ba mai ikon rufewa. Abin da ya rufe kuwa ba mai ikon buɗewa.
Saboda haka ya 'yan'uwana, ƙaunatattuna, waɗanda nake bege, ku da kuke abin farin cikina da abin taƙamata kuma, ku dage ga Ubangiji, ya ku ƙaunatattuna.
“Da a ce ina da wanda zai kasa kunne gare ni, Da sai in sa hannu a kan abin da na faɗa, Allah kuwa Mai Iko Dukka ya amsa mini. “Da ƙarar da maƙiyana suke kai ni, a rubuce ne,