wadda ake yabo a kan kyawawan ayyukanta, wadda kuma ta goyi 'ya'ya sosai, ta yi wa baƙi karamci, ta wanke ƙafafun tsarkaka, ta taimaki ƙuntatattu, ta kuma nace wa yin kowane irin aiki nagari.
Ku ci abincinku tare da mayunwata, ku kuma shigo da matalauta, marasa mahalli a cikin gidajenku. Idan kuma kun ga wanda yake tsirara, ku sa masa sutura, kada kuma ku ɓoye fuskokinku ga 'yan'uwanku.