Domin kuwa ko da yake sun san da Allah, duk da haka ba su ɗaukaka shi a kan shi Allah ne ba, ba su kuma gode masa ba. Sai tunaninsu ya wofince, zuciyarsu marar fahimta kuma ta duhunta.
Har yanzu suna ta ƙara yin zunubi, Suna yi wa kansu gumaka na zubi, Da gwaninta sukan yi gumaka da azurfarsu, Dukansu aikin hannu ne. Sukan ce, “Ku miƙa wa waɗannan hadayu!” Mutane sukan sumbaci siffofin maruƙa.
Ya zama daidai kamar mutum ya ci toka. Manufarsa ta wauta ta ɓatar da shi, har ba yadda za a iya taimakonsa. Ba zai iya ganewa ba, gunkin da ya riƙe a hannunsa ba allah ba ne ko kaɗan.
Ku yi mubaya'a da Ɗan, Idan kuwa ba haka ba zai yi fushi da ku, za ku kuwa mutu, Gama yakan yi fushi da sauri. Albarka ta tabbata ga dukan masu zuwa gare shi neman mafaka!
“Idan ɗan'uwanka, wato ɗan mahaifiyarka, ko ɗanka, ko 'yarka, ko ƙaunatacciyar matarka, ko amininka ya rarrashe ka a asirce, yana cewa, ‘Bari mu tafi mu bauta wa gumaka waɗanda ku da ubanninku ba ku san su ba,’
Ku lura fa, sa'ad da kuka dubi sama, kuka ga rana, da wata, da taurari, da dai dukan rundunar sama, don kada fa ku jarabtu, ku yi musu sujada, ko ku bauta musu. Ubangiji Allahnku ya sa waɗannan saboda dukan al'ummai.
Ya kuma kai ni farfajiya ta can cikin Haikalin Ubangiji. Na ga mutum wajen ashirin da biyar a ƙofar Haikalin Ubangiji a tsakanin shirayi da bagade, suka juya wa Haikalin Ubangiji baya, suka fuskanci wajen gabas, suna yi wa rana sujada.