Amma Ibraham ya ce, ‘Ɗana, ka tuna fa, a zamanka na duniya ka sha duniyarka, Li'azaru kuwa ya sha wuya. Amma yanzu daɗi ake ba shi, kai kuwa kana shan azaba.
Ya faɗa musu darajar wadatarsa, da yawan 'ya'yansa, da yawan matsayin da sarki ya girmama shi da su, da yadda sarki ya ciyar da shi gaba fiye da sarakuna da barorin sarki.
Yana da tumaki dubu bakwai (7,000), da raƙuma dubu uku (3,000), da shanu dubu guda (1,000), da jakuna ɗari biyar. Yana kuma da barori masu yawan gaske, don haka ya fi kowa a ƙasar gabas arziki nesa.
Ai, don ka kiyaye shi ne, shi da iyalinsa, da dukan abin da yake da shi. Ka kuma sa wa duk abin da yake yi albarka, ka kuwa ba shi shanun da suka isa su cika dukan ƙasan nan.
Hezekiya kuwa ya marabci manzannin, ya kuma nunnuna musu dukiyarsa, wato azurfa da zinariya, da kayan yaji da na ƙanshi, da dukan kayayyakinsa na yaƙi. Ba abin da bai nuna musu ba a ɗakunan ajiya, da ko'ina a mulkinsa.