“Duba, ga mutumin da bai dogara ga Allah Don ya sami zaman lafiyarsa ba. A maimakon haka, sai ya dogara ga wadatarsa. Yana neman zaman lafiyarsa ta wurin muguntarsa.”
Masu dukiyar duniyar nan kuwa ka gargaɗe su kada su nuna alfarma, kada kuwa su dogara da dukiya marar tabbata, sai dai ga Allah, wanda yake ba mu kome a yalwace don mu ji daɗinsa.
Ai, son kuɗi shi ne tushen kowane irin mugun abu. Don tsananin jarabar kuɗi kuwa waɗansu mutane, har sun bauɗe wa bangaskiya, sun jawo wa kansu baƙin ciki iri iri masu sukar rai.
Saboda haka, sai ku kashe zukatanku ga sha'awace-sha'wacen duniya, wato fasikanci, da aikin lalata, da muguwar sha'awa, da mummunan buri, da kuma kwaɗayi, wanda shi ma bautar gumaka ne.
Yakubu ya ji 'ya'yan Laban suna cewa, “Yakubu ya kwashe dukan abin da yake na mahaifinmu, daga cikin dukan abin da yake na mahaifinmu kuma ya sami dukiyarsa.”