Abimelek kuwa ya kira Ibrahim, ya ce masa, “Me ke nan ka yi mana? Wane laifi na yi maka, da za ka jawo bala'i mai girma haka a kaina da mulkina? Ka yi mini abin da bai kamata a yi ba.”
Bai fi ni iko cikin gidan nan ba, ba kuma abin da ya hana mini sai ke kaɗai, domin ke matarsa ce. Ƙaƙa fa zan aikata wannan babbar mugunta, in yi wa Allah zunubi?”