Saboda haka zan ba da matansu ga waɗansu, Gonakinsu kuma ga waɗanda suke cinsu da yaƙi, Saboda tun daga ƙarami har zuwa babba Kowannensu yana haɗamar cin muguwar riba, Tun daga annabawa zuwa firistoci Kowannensu aikata ha'inci yake yi.
Kowane ɗan farin da yake ƙasar Masar zai rasu, daga ɗan farin Fir'auna wanda zai hau gadon sarautarsa, har zuwa ɗan farin kuyanga wadda take niƙa, da dukan ɗan farin shanu.