Yara sukan tara itace, iyaye maza sukan haɗa wuta, iyaye mata sukan kwaɓa ƙullu don su yi wa gunkin nan wadda ake kira sarauniyar sama, waina. Sukan kuma miƙa wa gumaka hadayu na sha domin su tsokane ni.”
Dakiki yakan yi maganar wauta ya kuma yi tunanin mugayen ayyukan da zai aikata. Abin da dakiki yakan aikata da abin da yakan faɗa, duk ɓatanci ne ga Allah, bai kuwa taɓa ciyar da masu jin yunwa ba, ko ya ba masu jin ƙishi ruwa su sha.