7 Suka yi ta kuka a jeji, Suka taru wuri ɗaya a cikin sarƙaƙƙiya.
7 Suka yi ta kuka kamar dabbobi a jeji, suka taru a ƙarƙashin sarƙaƙƙiya.
Idan dakikan mutane sa yi hikima, To, jakunan jeji ma sa yi irin hali na gida.
“Idan jaki ya sami ciyawar ci, muradinsa ya biya, In ka ji saniya ta yi shiru, tana cin ingirici ne.
Zai zama mutum ne mai halin jakin jeji, hannunsa zai yi gāba da kowane mutum, hannun kowane mutum kuma zai yi gāba da shi. Zai yi zaman magabtaka tsakaninsa da 'yan'uwansa duka.”
Sai a kwazazzabai suke zama Da a ramummuka da kogwannin duwatsu.
Mutane ne marasa hankali marasa suna! Aka kore su daga ƙasar.
suna cike da ƙayayuwa, ciyayi sun sha kansu, katangar dutse da take kewaye da su ta faɗi.