5 Aka kore su daga cikin mutane, Suka yi ta binsu da ihu kamar yadda ake yi wa ɓarawo,
5 An kore su daga cikin mutanensu, aka yi musu ihu kamar ɓarayi.
Za a kore ka daga cikin mutane zuwa jeji ka zauna tare da namomin jeji. Za ka ci ciyawa kamar sa, za ka jiƙe da raɓa har shekara bakwai cur, sa'an nan za ka sani Maɗaukaki ne yake sarautar 'yan adam, yakan kuma ba da ita ga wanda ya ga dama.
Ka sa 'ya'yansa su rasa gidan zama, su riƙa yawon bara. Ka sa a kore su daga kufan da suke zaune!
Sukan tsinki ganyaye masu ɗaci na jeji su ci, Sukan ci doyar jeji.
Sai a kwazazzabai suke zama Da a ramummuka da kogwannin duwatsu.