4 Sukan tsinki ganyaye masu ɗaci na jeji su ci, Sukan ci doyar jeji.
4 A cikin jeji suna tsinkar ganyaye marasa daɗi, jijiyoyin itacen kwakwa ne abincinsu.
Har ma ya so ya cika cikinsa da kwasfar da aladu suke ci, amma ba wanda ya ba shi wani abu
Sai Amos ya amsa ya ce, “Ni ba annabi ba ne. Wannan ba aikina ba ne. Ni makiyayi ne, mai kuma lura da itatuwan ɓaure.
Iliya ya yi tafiyarsa yini guda cikin jeji, ya tafi ya zauna a gindin wani itace ya yi roƙo domin ya mutu, yana cewa, “Yanzu ya isa haka, ya Ubangiji, ka karɓi raina, gama ban fi kakannina ba.”
Saboda rashi da matsananciyar yunwa sun rame, Sai gaigayar ƙasa suke yi da dare, a cikin kufai.
Aka kore su daga cikin mutane, Suka yi ta binsu da ihu kamar yadda ake yi wa ɓarawo,