Idanuna sun dushe saboda kuka, Raina yana cikin damuwa. Zuciyata ta karai saboda halakar mutanena, Gama 'yan yara da masu shan mama Sun suma a titunan birnin.
“Ka duba, ya Ubangiji, ina shan wahala, Raina yana cikin damuwa, Zuciyata tana makyarkyata saboda tayarwata. A titi takobi yana karkashewa, A gida kuma ga mutuwa.
Ashe, Ifraimu ba ƙaunataccen ɗana ba ne? Ashe, shi ba ɗan gaban goshina ba ne? A duk lokacin da na ambace shi a kan muguntarsa Nakan tuna da shi da ƙauna. Saboda na ƙwallafa zuciyata a kansa, Hakika zan yi masa jinƙai, ni Ubangiji na faɗa.
Ubangiji ya ce wa Musa, “Tashi da sassafe ka sami Fir'auna a daidai lokacin da ya fita za shi rafi, ka ce masa, ‘Ni Ubangiji na ce ka saki jama'ata domin su yi mini sujada.