Biblia Todo Logo
အွန်လိုင်း သမ္မာကျမ်းစာ

- ကြော်ငြာတွေ -




Ayuba 30:25 - Littafi Mai Tsarki

25 Ashe, ban yi kuka saboda wanda yake shan wahala ba? Ashe, ban yi ɓacin rai saboda matalauta ba?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ

Sabon Rai Don Kowa 2020

25 Ashe ban yi kuka domin waɗanda suke cikin damuwa ba? Ko zuciyata ba tă yi baƙin ciki domin matalauta ba?

အခန်းကိုကြည့်ပါ။ ကော်ပီ




Ayuba 30:25
20 ပူးပေါင်းရင်းမြစ်များ  

Ku taya masu farin ciki farin ciki, masu kuka kuwa ku taya su kuka.


Amma idan ba za ku ji ba, Raina zai yi kuka a ɓoye saboda girmankanku, Idanuna za su yi kuka ƙwarai, za su zub da hawaye, Domin an kai garken Ubangiji zuwa bauta.


Kamar yadda yake a rubuce cewa, “Ya ba gajiyayyu hannu sake, Ayyukansa na alheri madawwama ne.”


Da ya matso kusa, ya kuma hangi birnin, sai ya yi masa kuka,


Saboda haka, ya sarki, sai ka karɓi shawarata, ka daina zunubanka, ka yi adalci. Ka bar muguntarka, ka aikata alheri ga waɗanda ake wulakantawa, watakila za a ƙara tsawon kwanakinka da salama.”


Daidai ne a rama alheri da mugunta? Duk da haka sun kafa wa raina tarko. Ka tuna yadda na tsaya a gabanka, Na yi maganar alheri a kansu, Domin ka janye fushinka daga gare su.


Idan kana tara dukiya ta wurin ba da bashi da ruwa kana kuma ƙwarar jama'a, dukiyarka za ta koma ga wanda yake yi wa talakawa alheri.


Sa'ad da ka bayar ga matalauci kamar ka ba Ubangiji rance ne, gama Ubangiji zai sāka maka.


Wanda ya yi wa matalauci ba'a, Mahaliccinsa yake yi wa zargi. Idan kana murna da hasarar wani, za a hukunta ka.


Wanda ya zalunci matalauci ya zargi Mahaliccinsa ke nan, amma nuna alheri ga matalauci yin sujada ne.


Idan kana so ka zama mai farin ciki, sai ka nuna alheri ga matalauci. Zunubi ne ka raina kowane mutum.


Ka cece ni, ya Ubangiji, Ba sauran mutanen kirki, Ba kuma za a sami amintattun mutane ba.


Sukan hana matalauta samun halaliyarsu, Sukan tilasta wa masu bukata su gudu su ɓuya.


Domin sa'ad da matalauta suka yi kuka, ni nake cetonsu, Nakan taimaki marayu waɗanda ba su da mai taimako.


Ni mahaifi ne ga matalauta, Nakan bincika don in warware al'amarin da ya dami baƙi.


Ko mutanen da suke cikin alfarwata ba wanda zai ce, Ga wani can da bai ƙoshi da nama ba.


ကြှနျုပျတို့နောကျလိုကျပါ:

ကြော်ငြာတွေ


ကြော်ငြာတွေ