Dukan masu ƙaunarku sun manta da ku, Ba su ƙara kulawa da ku, Domin na yi muku bugu irin na maƙiyi. Na yi muku horo irin na maƙiyi marar tausayi, Domin laifofinku masu girma ne, Domin zunubanku da yawa suke.
Sai Elihu, ɗan Barakel, mutumin Buz, daga cikin iyalin Arama, ya husata, yana fushi da Ayuba saboda ya baratar da kansa, bai bari Allah ya baratar da shi ba.