19 Allah ya jefar da ni cikin laka, Na zama kamar ƙura ko toka.
19 Ya jefa ni cikin laka, na zama ba kome ba sai ƙura da toka.
Saboda haka na ga ni ba kome ba ne, Na tuba, ina hurwa da ƙura da toka.”
Allah ya jefa ni a kwatami, Har tufafina ma suna jin kunyata.
Ibrahim ya amsa ya ce, “Ga shi, na jawo wa kaina in yi magana da Ubangiji, ni da nake ba kome ba ne, amma turɓaya ne da toka.
Sai suka ɗauki Irmiya suka saka shi a rijiyar Malkiya ɗan sarki, wadda take gidan waƙafi. Suka zurara Irmiya a ciki da igiya. Ba ruwa a rijiyar, sai dai lāka, Irmiya ya nutse cikin lākar.
Ka cece ni daga nutsewa cikin wannan laka, Ka kiyaye ni daga maƙiyana, Daga kuma wannan ruwa mai zurfi.
Ayuba ya je ya zauna kusa da juji ya ɗauki tsingaro ya yi ta sosa ƙurajen.