Ba za ka iya gafarta mini zunubina ba? Ba za ka kawar da kai ga muguntar da na aikata ba? Ba da daɗewa ba zan rasu in koma a ƙura, Lokacin da ka neme ni ba za ka same ni ba.”
Ba su kwanta kusa da manyan jarumawan da aka kashe ba, waɗanda suka tafi lahira da makamansu, aka yi musu matasan kai da takubansu, aka rufe ƙasusuwansu da garkuwoyinsu, gama manyan jarumawan nan sun baza tsoro a duniya.