Kaitona, ya mahaifiyata, da kika haife ni, mai jayayya mai gardama da kowa cikin dukan ƙasar! Ban ba da rance ba, ba kuma wanda ya ba ni rance, duk da haka dukansu suna zagina.
Bari su zama kamar katantanwu waɗanda sukan narke su yi yauƙi, Allah ya sa su zama kamar jinjirin da aka haifa matacce. Wanda bai taɓa ganin hasken rana ba.
Mai yiwuwa ne mutum ya haifi 'ya'ya ɗari ya kuma yi tsawon rai, amma kome tsawon ransa ba wani abu ba ne idan ba shi da farin ciki, bai kuma sami kyakkyawar binnewa ba. Sai na ce, gara jaririn da aka haifa matacce da shi.
Gama bai taɓa ganin hasken rana ba, bai kuma san abin da ake ce da shi rai ba. Amma duk da haka ya dai huta, fiye da mutumin da bai more wa rai ba, ko da ya shekara dubu biyu. Duk da haka dukansu wuri ɗaya za su tafi.