Dukan jama'a suka ce, “Mu ne shaidu, Ubangiji yă sa matar da za ta zo gidanka ta zama kamar Rahila da Lai'atu waɗanda suka gina gidan Isra'ila. Allah ya arzuta ka cikin Efrata, yă sa ka yi suna a cikin Baitalami,
Ebed-melek, bābā, mutumin Habasha, wanda yake a gidan sarki, ya ji labari sun saka Irmiya a rijiya. A lokacin nan, sarki yana zaune a Ƙofar Biliyaminu.
Mala'ikun nan biyu kuwa suka isa Saduma da maraice, Lutu kuwa yana zaune a ƙofar Saduma. Sa'ad da Lutu ya gan su sai ya miƙe ya tarye su. Sai ya yi ruku'u a gabansu.